Mata Basu Samun Damar Da Ta Dace

Barrister Badiha Abdullahi Mu'azu mai rajin kare hakin bil-Adam

Kamar yadda muka alkwarta masu sauraronmu a makon da ya gaba mun waiwayi batun nan ne na daidaito tsakani maza da mata , inda kuma muka zanta da wasu mata mabanbanta suka kuma bayyana mana ra’ayoyinsu dangane da batun daidaito.

Idan mai sauraro zai iya tunawa mu sha alwashin zantawa da masu rajin kare hakkin bil Adama, inda muka zanta da Barrister Badiha Abdullahi Mu’azu, Lauya mai zaman kanta a Kano, akan daidaito ta ce kawo yanzu idan ana batun daidaito to lailai mata basa samun damar da ta dace a basu ba , a mafi yawan lokuta ana daukar gazawarsu a matsayin wata tawaya.

Ta kara da cewa rashin daidaiton dai ya samo asali ne bisa ga al’ada, duk da cewa adinin musulci bai bambanta mussamam a bangarori neman ilimi da rufawa kai asiri da sauransu .

Al’umma ke dakile ‘yancin mata mussamam idan wani abu ya taso a dangi sai a rika cewa ai mace ce ba zata iya ba, ba’a la’akari cewa indai ba’a ba manta damar neman ilimi ba, da kuma basu damar yin amfani da ilimin da zuka samu daidai gwargwado me zai hana a bar mate su rike wasu madafun iko ko a basu damar taka muhimmiyar rawa a al’ummarsu.

Barista Badiha ta ce kundin tsarin ,mulkin Nijeriya bai yarda da rashin daidaito tsakanin Maza da Mata ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Basu Samun Damar Da Ta Dace - 4'39"