A Najeriya Mata Sun Yi Zaman Makoki Domin Tunawa Da Madam Salome

Ana ci gaba da gudanar da bukukuwan Kwanaki 15 da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya domin ganin an kawar da cin zarafin mata a Duniya.

Mata sun nuna bakin cikinsu akan yadda shugabar mata ta jamiyar PDP Madam Salome Acheju Abuh ta mutu a sakamakon cinna wa dakin ta wuta a lokacin da take ciki, har ta kone kurmus, wanda wadansu da ba a san ko su wanene ba suka yi a lokacin da ake zaben gwamna a ihar Kogi.

Matan sun yi tattaki na musamman daga cibiyar mata zuwa ofishin Kula da Harkokin Mata ta Abuja sanye da fararen riguna masu dauke da sakonni daban daban na nema wa Salome hukunci cikin gaggawa.

A cikin mata da suka yi wannan tattaki akwai diyar ta mai suna Ekojonwa Courage Tevershima wacce ta bayyana mahaifiyar ta a matsayin mace mai kamar maza goma, mai raha da yin haba-haba da mutane ko da ba ta san su ba.

Courage ta ce abin da ya faru da mahaifiyar ta ba abu ne da bai dace ba kuma tana neman shugaba Mohammadu Buhari ya sa baki saboda a nemo wadanda suka yi wanan mumunan aiki a hukunta su da hukunci mai tsanani, sanan a kula da iyalin da Salome ta bari a baya.

Daya cikin masu shirya tattakin Salma Abdulwahid, ta ce sun yi wannan zaman makokin ne domin su nuna wa Salome kauna tare da yin tir da yadda ta mutu a lokacin zabe, Salma ta ce zabe ba yaki ba ne, gwamnati ta dauki mataki saboda bai kamata a sake ganin an sami salwantar da ran wata mace a kasar nan gaba.

Ita ma Ministar Kula da Ma'aikatar Mata Dame Pauline Talen ta tabbatar wa matan cewa shugaba Mohammadu Buhari ya riga ya bada umurnin a nemo wadanda suka yi wanan aika aika din, domin a hukunta su, kuma ta ce da shi da mataimakinsa Forfesa Osinbajo da Uwargidansa Aisha Buhari za su jajirce domin ganin a hukunta duk wanda aka kama da laifi wajen kashe Madam Salome.

Ranar 10 ga wanan wata na Disamba ne ake sa ran mata za su kamalla bukuwan nasu.