Mata A Najeriya Na Ci Gaba Da Jan Hankali Akan Kare Kananan Yara

Wasu mata, musamman iyaye da kuma masu zurfin ilimi a Najeriya sun takarkare akan ci gaba da jan hankalin al'umma da hukumomi game da bukatar a kara daukar matakan hana satar yara da sayar da su ko kuma tura su bauta wasu sassan kasar.

Wannan lamarin na zuwa ne bayan gano wasu yara 9 da rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jiyar Kano ta yi, bayan da aka sace su a jihar Kano aka kai su yankin kudu maso gabashin kasar.

Farfesa Hauwa Imam, ta jami’ar Abuja,ta ce illar da a ka yi wa yaran sai an yi da gaske kafin a sake dawo mu su da tarbiyyar su ta asali.

Amma a na ta bangaren wata uwa daga Kano Maryam Mamman Nasir, ta ce su ma iyaye su na da nasu laifin na rashi kula da ‘ya’yan su.

Shi kuma malam Kabiru Gwamgwazo, jigo ne a wata kungiyar kare muradan Kanawa, ya karfafa bukatar sanin bayanai akan baki da su ke zama a kowacce jiha da nufin gano masu muguwar manufa a saukake.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata A Najeriya Na Ci Gaba Da Jan Hankali Akan Kare Kananan Yara