Masunta Sun Baiwa Marada Kunya A Bikin Kamun Kifin Geriyo

Bikin Kamun Kifin Geriyo

Bikin kamun Kifin Geriyo na bana ya yi Albarkar Kifi sai dai babu kudade a hannun jama'a

An gudanar da bikin kamun kifin bana na tafkin Geriyo, dake masarautar Adamawa, a arewa maso gabashin Najeriya, inda masunta suka hallara daga ciki da wajen jihar.

Sai dai a bana matsalar rashin kudi ya so ya jawo cikas inda masunta da masu sayar da kifin suka koka da rashin kasuwa, wanda haka ke da nasaba da rashin kudin da ma’aikata ke fama dashi.

A bana ma daruruwan masunta ne da kuma masu saya suka cika a bikin kamun kifin na Geriyo, a wani yanayi na ban sha’awa.

Geriyo dake karkashin masarautar Adamawa, wani waje ne da ake noman rani musaman noman shinkafa, kuma duk shekara masunta kan yi turuwa don zuwa bikin kamun kifin inda kowa ke fafutukar samun rabon sa.

A shekarun baya dai, akan cika inda matan aure kan nuna fushinsu ga duk mijin da bai zo da kifin Geriyo ko na Njuwa ba,to sai dai kuma ba kamar shekarun bayan ba,matsalar karancin kudi ya kawo tsaiko a bana.

Mallam Abdulrazaq Abubakar dake zama Sarkin ruwan Geriyo ya bayyana muhimmancin wannan kamun kifi da ake yi a Geriyo da cewa yana da dadadden tarihi a jihar.

Shima da yake Karin haske shugaban kungiyar masuntan jihar Adamawa Mahmud Ali Kano ya koka ne da abinda ya kira halin ko in kula da hukumomin ke nunawa ga harkar raya madatsun ruwa dake taimakawa wajen samun kifi.

Shugaban na kungiyar masuntan ya yi kira ga gwamnatin jihar data taimaka wajen raya tafkin Geriyon, ganin cewa wasu tafkunan da ake dasu a baya sun kafe,kamar Njuwa wanda hakan yace zai taimaka wajen samar da aikin yi ga matasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Masunta Sun Baiwa Marada Kunya A Bikin Kamun Kifin Geriyo - 3'41"