A kasar Hunduras, daruruwan masu zanga-zanga ne suka rurrufe hanyoyi da za’a bi don zuwa binne wadanda suka mutu a sanadiyyar COVID-19.
Masu zanga-zanga daga garuruwa kusan 24 ne suka jera duwatsu da itatuwa akan manyan tituna a gabashin birnin Tegucigalpa, don hana kawo gawarwakin garuruwansu saboda kada iyalan mamatan wadanda suma ta yiwu suna dauke da cutar su yada musu.
Daya daga cikin masu zanga-zangar Elevia Olivia ta na cewa shugaban kasar cikin fushi “ba mu so ya turo mana masu dauke da cutar, su kawo mana gawarwaki su binne a garuruwanmu. Muna da iyalai da yawa bamu so su kamu.”
Mataimakin Ministan lafiya Roberto Cosenja ya bayana cewa, hukuma zata wayar da kan al’umma akan yadda cutar ke yaduwa kuma za a tabatar da tsaro don a samu damar binne mamatan.
Kasar ta Hunduras na da kimanin wadanda ke dauke da cutar 1,000 kuma 82 suka mutu a sanadiyyar cutar.