Masu Zanga-zanga a Bamako Sun Bukaci Shugaba Keita Ya Yi Murabus

Masu zanga-zanga a Mali

Akalla mutum daya ya mutu a yayin da masu zanga-zanga a babban birnin Mali suka yi yinkurin mamaye wasu muhimman gine-ginen gwamnati da kuma toshe manyan hanyoyin birnin a ranar Juma’a 10 ga watan Yuli, suna yin kira ga Shugaba Ibrahim Boubakar Keita akan ya yi murabus.

Gidan talabijin din Mali na ORTM ya dakatar da aiki bayan da wasu masu zanga-zanga suka tattaru a wajen ginin.

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita

Wani bidyo da sashen Bambara na Muryar Amurka ya dauka daga Bamako babban birnin kasar, ya nuna yadda dubban masu zanga-zanga suka taru a wajen ginin majalisar dokokin kasar, suna bukatar Keita ya yi murabus.

An kuma samu rahoton jami’an kwantar da tarzoma na kasar sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da suka dinga jefa duwatsu kan ginin majalisar dokokin kasar.