A ranar Juma’a masu tada kayar baya suka kai hari kan birnin Aleppo, birni na biyu mafi girma a Syriya, inda suka tayar da motoci biyu dauke da bamabamai, yayin da suka yi arangama da dakarun gwamnati a yankin Arewacin birnin, cewar masu sa ido akan yakin kasar ta Syriya.
Wannan shine karo na farko da dakarun adawa suka kaiwa birnin hari tun bayan shekarar 2016, lokacin da aka iza keyar su daga yankunan dake makwabtaka da yankin gabashin Aleppo, biyo bayan wani gangamin dakarun gwamnatin Syriya, da Rasha, Iran da sauran kawayen su, suka marawa baya.
Shaidun gani da ido a birnin Aleppo sun ce, mazauna yankunan dake makwabtaka daga bangaren Arewacin birnin sun rika arcewa, saboda harin makamai masu linzami da musayar wuta. Gwamnatin dai bata ce kala ba dangane da irin wuce makadi da rawa da masu tada kayar bayan keyi a birnin.
Rundunar dakarun Syriya ta fada cikin wata sanarwa a jiya Juma’a cewa, ta rika arangama da masu tada kayar baya a yankin kasar, ta yankin Aleppo da Idlib, inda suka lalata da dama daga cikin jiragen su marasa matuki da sauran manyan makamai. Rundunar ta sha alwashin dakile hare haren, ta kuma zargi masu tada kayar bayan da yada labaran karya game da hare haren.
Dubban masu tada kayar baya sun rika nausawa zuwa birnin Aleppo, tun bayan da suka kaddamar da wani gagarumin hari a ranar Laraba, inda suka kwace garuruwa da dama da kauyukan dake kan hanya.
Fadan ya balle ne, a yayin da kungiyoyin dake da alaka da Iran, da suka rika goya bayan dakarun gwamnatin Syriya tun a shekarar 2015, ke fama da nasu rigingimun a cikin gida.
Kungiyar sa ido kan hakkin bil’adama ta Syriya, dake sa ido kan yake yake, tace,a ranar Juma’a ne masu tayar da kayar bayan, suka tayar da motoci biyu masu dauke da bamabamai, a yankin Arewacin birnin.
Wani kwamandan yan tayar da kayar bayan, ya fitar da wani sakon murya a kafar sadarwar zamani, yana kira ga mazauna birnin da su ba dakarun hadin kai.
Kafar yada labaran Anadolu ta kasar Turkiyya ta ruwaito cewa, yan tada kayar bayan na bangaren yan adawa sun shiga tsakiyar birnin Aleppo a ranar Juma’a. Ta kara da cewa yan tada kayar bayan sun keta layin tsaron da dakarun gwamnati suka shata, ta bangaren Ahmadiyya na sabuwar Aleppo, da yankin Zahra ta bangaren wajen birnin.
Kafar ta kara da cewa, a yanzu yan tada kayar bayan na da iko da kimanin wurare 70 a yankin Aleppo da Idlib.