Jamhuriyar Nijar ta bukaci 'yan kasuwa daga kasashen waje su shigo kasar su saka jari a fannonin sufuri da tsaftace muhalli da kuma raya birane
WASHINGTON DC —
Bayan 'yankasuwan sun tattauna da shugaban kasar Mahammadou Issoufou a fadarsa tawagar shugabannin kamfanonin na Faransa ta sadu da 'yankasuwar Nijar.
Malam Musa Sidi Muhammad shugaban majalisar 'yanksuwar Nijar yace kasar Nijar ta shirya duk abun da ya kamata a yiwa 'yankasuwa na ciki da na waje masu zuwa saka jari. Tawagar manyan kamfanonin da suka zo daga Faransa sun gamsu cewa Nijar kasa ce da kowa mai neman saka jari zai so ya ziyarceta.
Da Faransa na yi dari dari da saka jari a Afirka amma tunda Nijar ta fara fita kasashen Asiya da Amurka Faransa din tana neman dawowa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5