Wani labari da jaridar Wall Street ta wallafa, ya cewa, ‘Masu ‘yan China sunyiwa kamfanonin wayar salula a Amurka kutse sannan sun sato bayanai daga na’urrorin gwamnatin tarayya inda ake addana bayanan wayar mutane da kotu ta bada izinin a tatsa.
Ya yiwu masu kutsen sun kwashe tsawon wattani suna tatsar bayanai daga na’urar da kamfanonin suke aikewa kotun bayanan da ta bukata daga gare su wanda ya shafi mu’amala ta waya na tsawon wattani, sannan jaridar ta kara da cewa masu kutsen sun kuma samu wasu bayanai akan bayanan mutane na internet.
Ma’aikatar harkokin wajen China ta mai da martini a ranar Lahadi, inda ta ce bata da wanta masaniya a game da satar bayan kamar yadda jaridar ta ruwaito, sannan kuma ta ce kagagaen labari Amurka ta kirkiro da zummar shafawa China kashin kaza.
A daidai lokacin da batun tsaron a kafafen yanar gizo yake dada zama babban kalubale ga kasashe a fadin duniya, babu abinda wannan mumunan matakin zai haifar ga yunkrin da akeyi don ganin an magance wannan kalubalen ta hanyar samun tattaunawa da hadin kai tsakanin kasashe, a binda ma’ikatar ta fada kenan cikin wata sanarwar da jaridar ta ce ta fitar .