Waiwaye a kan ayyukan da kwamitin tsaro na Security Governance Initiative, ya gabatar a fannin yaki da ta’addanci cikin watanni shidda da suke wuce domin tantance yadda za a sake bullowa matsalar, na cikin muhimman batutuwan da kusoshi a bangaren tsaron kasar jamhuriyar Nijer, tare da takwarorinsu na Amurka suka tattauna akai.
Kakakin wannan kwamiti, Kanar Mustapha, ya bayyana cewa sojojin na Amurka, suna da kwarewa wajan yaki da ‘yan ta’adda, dan haka wannan na daya daga cikin abubuwan da kasar ke bukata.
Mukaddashin jakadiyar Amurka a Nijer, ya bayyana gamsuwa da hadin kan da jami’an kasar ke bayarwa domin cimma ayyukan da kwamitin ya sag aba.
Harkokin tsaro lamari ne da yaki ci yaki cinyewa a jamhuriyar Nijer, dalilin haka ne jami’in fafutuka na kawance, Malam Salisu Amadu, ya yi kira ga magabatan koli da su sa ido.
Sai dai masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaron Nijer, na cewa yaki da ta’addanci sai dai a ce Allah-Sam-Barka.
Amurka na daya daga cikin kasashen da suka girke dakaru a jamhuriyar Nijer domin yaki da ta’addanci, dalilin Kenan da ya sa kasar ta bukaci Amurka ta kara yawan jiragen sama da zasu taimaka wajan sa ido a kan iyakar kasar da Mali, yankin da ‘yan bindiga saka hallaka dakarun Kasar ta Nijer da na Amurka 4.
Domin karin bayani, saurari rahoton Sule Mumuni Barma a nan.
Your browser doesn’t support HTML5