A cewar shugaban kungiyar Kwamared Samson Almuru, kungiyar ta koma ga kai kokenta ga Allah ta adu’o’i ganin hakan ta ya kasa cimma ruwa duk da koke-kokenta ga hukumomi da shugabannin jama’a na rashin biyan su hakkokinsu.
Shugaban ma’aikata na jihar Adamawa Barista Musa Kaibo, wanda ya tabbatar da wannan bashin ya baiwa tsoffin ma’aikatan hakuri yana mai cewa gwamnati na aiki akan wata sabuwar kudirin doka na biyansu hakkokinsu, ganin yadda gwamnati ta kasa biyansu daga kaso na kasafin kudinsu na shekara-shekara.
Wani dan fafatuka na kungiyar Kwamared Alyosus Sini, ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, cewa rabon da gwamnatin jihar Adamawa ta yi wa masu karbar fansho Karin kudi tun shekara ta 2003 sabanin tanadin da dokar kasa ta shekarar 1999 ta yi na Karin kudi tare da takwarorinsu dake aiki a duk lokacin da aka yi masu Karin albashi da kuma bayan duk shekaru biyar.
Wasu daga cikin masu jiran kudin sallamar ajiye aiki da na fansho da sashin Hausa na Muryar Amurka ya yi hira da su kan matakan da hukumar kula da fanshon ma’aikata na jihar Adamawa ta dauka na ragewa wadanda ke cikin halin rayuwa na matsi radadi ta hanyar kasa kudadensu gida uku zuwa hudu sun gwammace su barwa magadansu hakkokinsu.
Yayin da wasu ke tababa kan tallafin da gwamnati tarayya ta ce ta baiwa jihohi domin biyan bashin da ma’aikata ke binsu.
Bincike ya nuna sama da mutane dubu goma ke jiran tsammani na biyansu kudadensu na ritaya, adadin da ke karuwa a duk mako.
Your browser doesn’t support HTML5