Masu Karban Kudin Fansho A Jihar Bauchi Sun Koka.

  • Ladan Ayawa

Staff members of This Day newspaper sit outside, as workers barricaded the front office due to non payment of salaries in Lagos, May 10, 2013.

An kammala tantance maaikata da ‘yan fansho a jihar Bauchi amma kuma tantancewar ya bar baya da kura.

A jihar Bauchi da yawan maaikata hadi da ‘yan fansho basu samu albashin su ba.

Hakan ya bayyana ne biyo bayan biyan albashin watan da ya gabata. Alhaji Abugar shine shugaban ‘yan fansho a jihar Bauchi.Yace sunkai su kimanin mutane dubu 6 da basu samu albashin sub a.

Ga dai abinda ya shaida wa Abdulwahab Mohammed.

‘’Mutane masu karban fansho sun kai dubu 6 suna da ran su, sun hallata wasu kuma basu da karfin da zasu zo wasu ma sai an daga su, wasu ko sai an kwantar dasu wasu ma bayan gida ana karba musu a gidajen su akwai kuma wadanda suke da lafiyar su basu zo ba, basu da wani labari wani kuma ya dauka ma tantancewar da akeyi shirme ne.Anzo idan kana da BVN ma sai ace wai masu bincike sun bincika kai maaikacin bogi ne, kuma gaka da ran ka, wannannabu abin mamaki ne.’’

Shiko wani maaikacin gwamnatin jihar Bauchi yace suna watanni na ukku Kenan babu albashi.

‘’Gaskiya batun albashi a jihar Bauchi abin sai kara tabarbarewa yake yi, mutane sun gagara gane gaskiyan abubuwa ba cewa akayi a jihar Bauchi ba maaikatar bogi ba amma kuma maaikatar bogin da aka ce akwai su a Bauchi ya wuce hankali.’’

Sai dai da Abdulwahab ya tambaye shi ko ya samu albashin sa shine sai ya amsa da cewa.

‘’Ni ina cikin wata na biyu Kenan da ban samu albashi ba.’’

Wannanyanayin ba wai ya tsaya ga maaikata ne ba suma ‘yan kasuwa ta shafe su.

Ga Abdulwahab da ci gaban rahoton 2’44

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Karban Kudin Fansho A Jihar Bauchi Sun Koka. 2'44