Masu Haifuwa A Hannun Unguzoma Na Cikin Barazana A Zimbabwe

Shugaban Zimbabwe, EMMERSON MUNGAGWA

Mata a kasar Zimbabwe suna dogara da unguzomomi ala tilas sakamakon tabarbarewar tsarin kiwon lafiyar kasar kana suna haihuwa a cikin yanayi maras tsabta, lamarin da masana suka ce yana jefa iyaye mata da jariransu a cikin hatsarin kamuwa da cutuka.

Lokuta da dama akan tilasta wa kananan asibitoci rufewa, saboda ma’aikatan lafiya sun shiga yajin aikin neman karin albashi tun a watan Satumba.

Mata masu juna biyu, su na zuwa wurin ungunzoma suna haihuwar jariransu, a cewar Esther Zinyoro-Gwenya, wata ungunzoma da ke Mbare, daya daga cikin garuruwa masu fama da talauci a Harare.

Zinyoro-Gwenya mai shekaru 74, ta ce ta karbi haihuwa kusan 250 a watan Nuwamba.

Duk da yake ta ce dukkan matan da jariran su sun rayu, amma kuma yanayin na jefa su cikin hatsarin gaske na kamuwa da cutuka.

Haka kuma wannan alama ce ta tabarbarewar tsarin kiwon lafiya a kasar, in ji Dr. Tawanda Zvakada, na kungiyar likitocin kasar Zimbabwe.

Dr. Zvakada yace, lamarin kasar ta tsinci kanta a ciki a yanayin da mata suke haihuwa a wuraren da basu da kulawar tsabta babu dadi, hakan bai dace da tanadin hukumar lafiya ta duniya ba na wurin da ya cancanta a haifi yara.

Likitoci da ma’aikatan jiyya a kasar ta Zimbabwe, suna bukatar gwamnati ta samar da kayan aiki na zamani ga asibitoci da dakunan shan magani da suka tabarbare tare da tattalin arzikin kasar. Babban Bankin Duniya na sa ran harajin cikin gida na Zimbabwe zai yi kasa da kashi 7.5 bisa dari a shekarar 2019.

George Guvamatanga, Sakataren ma’aikatar kudi da ci gaban tattalin arziki, ya ce Harare na sane da matsalolin sha’anin kiwon lafiya, kuma gwamnati na kokarin shawo kan su.

Yanzu haka dai mata masu juna biyu a Zimbabwe suna iya kokarin da suke iya yi.

Ga rahoto na musamman a kan wannan batu:

Your browser doesn’t support HTML5

RAHOTO NA MUSAMMAN A KIWON LAFIYAR ZIMBABEW