Akalla garuruwa 17 ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa suka tarwtatsa a kananan hukumomin Rafi da Shiroro da ke cikin jihar Nejan Najeriya.
Wannan al’amari ya sa dubban mazauna garuruwan zuwa yin gudun Hijira a garuruwan Kagara da Pandogari domin tsira da Rayukkansu.
Muryar Amurka ta zanta da wasu a sansanin gudun hijirar da ke garin Kagara sun ce tashin hankali ne ya sa tilas suka bar garuruwan domin a kullum sai ‘yan bindigar sun kawo masu hari.
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda jihar ta Neja akan batun ‘yan bidigar ya cutura duk da cewa an buga wayar kakakin ‘yan sandar DSP Abubakar Dan Inna tare da tura sakon tes.
Sai dai hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja ta ce ta kai tallafin barguna da tabarmai da kayan abinci ga ‘yan gudun hijirar.
Shugaban Hukumar Alhaji Ibrahim Inga, ya tabbatar da cewa masu gudun hijirar sun kai kimanin 4000.
Saurari rahoton Mustapha Nasir Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5