Masu Garkuwa Da Limamin Coci Sun Bukaci Miliyan 30

Wata mujami'a a jihar Kano Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, wadanda suka yi garkuwa da wani limamin coci da da wasu mabiyansa 14, sun tuntubi iyalan mutanen da suke garkwau da su.

Kafofin yada labarai sun ruwaito shugaban kungiyar Kiritoci ta CAN reshen jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Joseph Hayab ya tabbatar da wannan lamari, inda ya ce masu garkuwan sun tuntubi iyalan tare da neman kudin fansa har naira miliyan 30.

Wasu bayanai sun yi nuni da cewa, masu garkuwa da mutanen, sun yi maza-maza sun kashe wayarsu, bayan da suka tuntubi iayalan, a wani mataki da ake ganin dabara ce ta kada a bibiyi inda suke.

An sace mutanan ne a mujami’ar ECWA da ke Dankade a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, daga cikin wadanda aka yi garkuwan da su, har da diyar limamin cocin.

Matsalar garkuwa da mutane musamman a wasu sassan arewacin Najeriya, ta zama ruwan dare, lamarin da ya jefa dumbin jama’a cikin yanayi na rashin tabbas kan tsaronsu.

A ‘yan kwanakin nan, mahukunta sun yi ikrarin cafke akalla masu garkuwa da mutane 93 a sassan arewacin kasar, amma duk da haka, wasu na ganin lamarin kara ta’azzara ke yi.