Masu Gabatar Da Kara A Argentina Sun Nemi Hukuncin Daurin Shekaru 12 Ga Mataimakiyar Shugaban Kasa Fernandez

Mataimakiyar shugabar kasar Aregentina, Cristina Fernandez

“Wannan abun da ke gabanmu, shi ne al’amari mafi girma na almundahana da wannan kasa ta taba gani,” a cewar mai gabatar da kara Diego Luciani.

WASHINGTON D.C.: Masu gabatar da kara, sun bukaci wani alkali ya zartas da hukuncin daurin shekaru 12 ga Mataimakiyar Shugaban kasar Argentina, Cristina Fernandez, tare da haramta ma ta rike duk wani mukamin gwamnati, saboda zargin cewa ta jagoranci wata harkar muna-muna, ta bayar da kwangiloli na ayyukan gwamnati ga abokai da na kusa da ita.

“Wannan abun da ke gabanmu, shi ne al’amari mafi girma na almundahana da wannan kasa ta taba gani,” a cewar mai gabatar da kara Diego Luciani.

Diego ya bayyana hakan ne a jawabinsa na karshe a shari’ar da ake ma Fernandez, wadda ta taba kasancewa shugabar Agentina daga 2007 zuwa 2015, kafin ta zama Mataimakiyar Shugaban kasa daga 2019 zuwa yanzu.

Kasar ta yi asarar dala biliyan 1 sanadiyyar wannan almundahanar, a cewar Luciani.

Tsohuwar Shugabar ta kekeshe kasa ta ce sam ba ta aikata wadannan abubuwan da ake tuhumarta da su ba, a wannan shari’ar da aka kwashe shekaru uku ana yi.