Tun kafin majalisar dokokin Nijar ta amince da kasafin kudin shekarar 2018, kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka gargade ta da kada ta amince da shi saboda wasu dokokin da kasafin ya kunsa da suke ganin za su cutar da talakawan kasar.
To sai dai majalisar ba ta yi aiki da shawarwarin kungiyoyin farar hula da na 'yan rajin kare hakkin dan Adam ba.
"Bayan zamanta (majalisa) ta yi na'am da kasafin," inji Suraji Isa.
A cewar Suraji Isa duk da cewa bakin gwamnati da na 'yan majalisa ya zo daya akan kasafin wadanda suke mulki a kansu, kimanin mutane miliyan 20, basu yadda ba.
Ya ce saboda haka yanzu suka ja daga da gwamnati da 'yan majalisa. Ya ce a cikin kasafin kudin za'a zalunci talaka da kasar gaba dayanta.
Amma a nasa ra'ayin, Inusa Ona, wani dan farar hula yana cewa duk wani cece-ku-ce akan kasafin kudin shekarar 2018 ya kare, zartas da abin da kasafin ya kunsa shi ne gwamnati za ta sa gaba.
Ya ce kuma musanta abubuwan da aka ce an saka cikin kasafin kudin.
Sai dai kungiyoyin da suke adawa da kasafin sun sha alwashin fantsama kan hanyoyi su nuna rashin amincewarsu tare da nufin tankwaso gwamnati ta canza ra'ayi.
Ga rahoton Sule Barma da karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5