A Najeriya rahotanni daga jihar Gombe na nuni da cewar mutanen da aka killace saboda kamuwa da cutar coronavirus, da yanzu haka su ke kwance a asibitocin garin Kwandon dake karamar hukumar Yamaltu Deba, da kuma asibitin koyarwa na garin Gombe, sun gudanar da tarzoma da zanaga-zanga, inda suka banke kofar dakin wurin da suke a killace, suka fantsama zuwa ciki gari.
Masu tarzomar sun kawo cikas ga harkar zirga-zirgar ababen hawa da kuma tsayar da harkan kasuwanci a garuruwan.
Daya daga cikin mutanen da aka killace mai suna Ja’afaru Muhammad ya ce, sun gudanar da zanga-zangar ne sobada tun da aka killace su a asibitin ba a basu wata kulawa ko magani.
Masu zanga-zangar sun sami goyon bayan jama’ar gari, inda suka fito don rufa musu baya, a cewar Wani daga cikin mutanen garin mai suna Rabi’u Munkaila.
Kwamishinan ma’aikatar lafya na jihar Gombe, kuma wakili a kwamitin yaki da cutar coronavirus, Dr. Ahmed Gana, ya yi bayani a hukumance da kuma fayyace hatsarin dake tattare da mutanen da suka gwamatsu da masu cutar ta coronavirus.
Ya ce "mutanen garin da suka fito suka cakudu da marar sa lafiyar ka iya janyo yaduwar cutar cikin sauri a cikin al'umma".
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5