Masu Jefa Kuria Suyi Karatun Ta Natsu

  • Ladan Ayawa

Wani mutum yana kada kuria a zaben majalisar tarayya

Yayin da zaben Najeriya ke kara matsowa kusa, manazarta na ganin lokavi yayi da masu jefa kuria yakamata suyi karatun ta natsu, musammam ganin yadda yan siyasar kasar ke kokarin canza akalar kasar.

Mr John Sheleng na kungiyar turaki Vanguard daya daga cikin wannan kungiyar dake fadakarwan yace dole mutane su kula da masu wa ingiza mai kantu ruwa.

‘’Shawara na musammam ga talakawa wadanda suke karkara shine mafita abinda zai zama muna alheri mu ajiye batun addini a gefe,kar ka yarda ranar zabe mutum yazo da kudi ranar zabe mutum yace zai gwada maka kudi domin ya sayi imanin ka, zai sayi imanin ka na lokaci kadan kazoo kana wahala na shekaru hudu masu zuwa nan gaba, wannan abinda nake so na janyo hankalin talakawa mu sani mu gujewa kwadayin kudi, mu jajirce wannan ya zama kamar yaki ne wanda an nemi al’umma gaba daya mu bada gudun mowa mu sauyin da muke bege a cikin yan kwanaki kadan da zamu same shi’’

Sai dai wani batu da kungiyoyin suka tabo shine na batun kin amincewa da sakamakon zabe musammam ga wadanda suke kan karaga, batun da su malam Yakubu na kungiyar sa ido a harkokin ci gaba nacewa kan madafan iko da wasu shugabannin Africa kanyi.

‘’Abinda shugabannin Africa su lura shine, su rika mutunta sakamakon zabe, idan aka kada kai tunda kasan wannan zaben anyi shi tsakani da ALLAH ne kawai ka muka ragamar mulki ka hankura ka tafi shi yin wannan ma zai jawo maka wani farin jinni, kaga a makwabtar mu nan Benin Republic lokacin zamanin Mathew Kerouko aka zo zabe aka kada shi ya sauka ya mika, wanda ya karba bayan shekaru 4 ya sake tsayawa sabo da baiyi wani abin kirki Mathew ya kada shi, kamar Ghana ma muna ganin irin wannan, jamiyyar adawa ta kada wadda ke kan mulki kaga idan akayi haka demokaradiyya ta dore, amma a yanayin da wadanda ke kan ulki idan sung aba zasu ci ba an dinga kawo kabli da baadi idan ba zasu samu ba to kowa ma ya rasa wannan ba zai kawo muna ci gaba a kasar nan ya kamata muyi wa kammu fada’’

Ga Ibrahim Abdul Azeez da Karin bayani


Your browser doesn’t support HTML5

Masu Zabe suyi Karatun Ta Natsu - 3'35"