Massimiliano: Rashin Dan Wasa Ronaldo, Ba Shine Koma Bayanmu Ba

Kocin kungiyar kwallon kafar Juventus Massimiliano Allegri

Mai horas da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Massimiliano Allegri ya bayyana cewa rashin nasarar da kungiyartasa tayi a satin daya gabata cikin gasar Siria A mako na 28, ba rashin dan wasa Ronaldo bane kamar yadda wasu ke tunanin ba.

Kulob din Genoa ce ta doke Juventus da ci 2-0 a gasar ta kasar Italiya, wanda hakan ya kawo karshen jerin nasarorin wasannin da Juventus ke bugawa a bangaren lig na Itaty a bana.

Yayin wasan na ranar Lahadi, kocin Allegri, ya hutar da dan wasansa Cristiano Ronaldo, wanda ya ciwa kungiyar dukkanin kwallaye uku da ta lallasa Atletico Madrid a gasar Zakarun Nahiyar Turai.

Sakamakon kin anfani da dan wasan a gasar Seria A wasu magoya bayan Juventus ke ganin ya taka rawa wajen rashin samun nasara a karawarsu Genoa.

Kungiyar ta Juventus ita take jagorantar gasar ta Seria A da maki 75, sai Napoli a matsayi na 2 da maki 60.

Bayan haka kuma har yanzu kungiyar tana cikin gasar kofin zakarun turai,
inda zata fafata da kungiyar Ajax a zagayen wasan daf da na kusa da na karshe Quarter Final.