Masharhanta Sun Yi Tsokaci Kan Jawabin Shugaba Buhari Akan Batun Tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari

Duk da kiraye-kirayen da masu fada a ji da masharhanta a harkokin tsaro da na yau da kullum ke yi ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari akan ya canza shugabannin rundunonin tsaron kasar da ake gani dabarunsu sun kare, Shugaban ya ce za a kara wa sojojin Nigeria da sauran jami’an tsaro kudade domin samun nasarar yakin da suke yi da ta’addanci.

A jawabin sa ga jama’ar Nigeria ranar Juma’a 31 ga watan Yuli, Shugaba Buhari ya kuma ce gwamnatinsa za ta himmatu wurin aikin kwamitin da ke binciken cin hanci da rashawa a gwamnatin da ta gabata da wadda ke ci a yanzu domin hukunta masu sama da fadi da dukiyar kasa.

Malam Nasiru Zaharadeen, kwararre a sha’anin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa, ya ce abu ne mai kyau a kara wa jami’an tsaro kudade amma kafin hakan ya kamata a bi ba’asin kudi sama da naira miliyan 200 da aka bayar a baya don magance matsalar tsaro, a kuma yi Nazari a ga idan ayyukan ta’addanci sun ragu a kasar ko a’a.

Game da batun yaki da cin hanci da rashawa kuma, Malam Nasiru ya ce ya kamata a ci gaba da binciken masu bincike da hukumomin da ake ganin sun rube, idan za a yi hakan tsakani da Allah, to tabbas za a koma kan hanyar yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata.

Dr. Ahmed Saleh, mai sharhi kan lamurran tsaro, shi kuma cewa ya yi a Najeriya bisa tarihi, babu Shugaban da ya kashe makudan kudade akan batun tsaro kamar Shugaba Buhari, amma duk da haka matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa, ya kuma kara da cewa duk karin kudin da za a yi muddin ba a canza shugabannin rundunonin sojan kasar ba, to zai yi wuya a ga wani canji ko ci gaba wajan kawar da kalubalen tsaro a Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Umar Farouk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Masharhanta Sun Yi Tsokaci Kan Jawabin Shugaba Buhari Akan Batun Tsaro