Masassharar Tsuntsaye a Najeriya

Ma'aikatan kiwon lafiyar dabbobi ke nan suna kawar da kajin da suka kamu da musasshara

An tabbatar da bullar musassharar a jihohi goma sha takwas a Najeriya inda lamarin ya fi kamari a Kano.

Suleiman Sambo daya daga cikin jami'an hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka ko USAID yayi bayani dangane da tallafin da hukumar ke bayar wa akan barkewar cutar.

Yace ana kokari aga cewa annobar za'a tsayar da ita a kuma yi maganinta. Yace cikin kashi dari na cutar da aka samu a Najeriya kashi hamsin a Kano ya ke. Yace duk wadanda aka gayyata wurin taron shawo kan cutar kwararru ne a bangaren kula da lafiyar dabbobi.

Sambo yace hukumar USAID idan ta horas da wadanda aka gayyata zasu je su koyawa na kasa dasu ta hakan za'a shawo kan cutar. Kamar yadda aka samu annobar a shekara 2006 bayan an bada bita da kayan aiki an shawo kanta wancan lokacin. Haka ma za'a shawo kanta wannan karon ma.

Gwamnatin Najeriya ta yaba da tallafin da hukumar USAID ta ke bayarwa domin kawar da matsalar. Wakilin gwamnatin tarayya din yace mutane na kiwon kaji ne domin abinci. Idan kuma cuta ta kammasu ai babu abinci ke nan. Ban da haka cutar tana kama bil Adama domin haka ya zama wajibi a kawar da ita.

Gwamnatin Kano tace tun lokacin da cutar ta bullo suka soma taka rawa domin kawar da ita.Su ne suke zuwa suna kwasan kaji da suka mutu su kai a gwadasu domin a san abun da za'a yi. A Kano inda ba'a zaton a kwai kaji za'a samesu. Yadda ake rukunin gidaje haka mutane suka yi rukunin gidajen kiwon kaji. Sabili da haka da zara daya ya kamu nan da nan cutar zata yadu.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Masassharan Tsuntsaye a Najeriya - 3' 32"