Kasashen Masar da Ethiopia da Sudan sun sanya hanu ta share fage kan yadda zasu yi amfani da ruwa daga kogin nilu, wanda ya baiwa Habasha damar ta ci gaba da aikin gina gagarumin madatsan ruwa data dukufa akai.
Ministan kula da harkokin ruwa na Ethiopia Alemeyehu Tegenu ya fadawa Sashen kasashe dake kuriyar Afirka na Muryar Amurka cewa, kasashen sun amince cewa ruwan kogin yana da muhimmanci ga duka kasashen uku, domin amfanin jama'a da kuma ayyukan ci gaba.
Yace ya dauki jami'ai daga kasashen uku watanni suna shawarwari domin bullo da yanayi ta fahimtar juna da suka hada da tsara manufofi bakwai, da suka hada da kaucewa mataki da zai yi matukar rauni ga kowace daya daga cikinsu, da kuma warware duk wata matsalar fahimtar juna cikin lumana. Kasashen zasu tantance sauran matakai a shawarwari da zasu yi nan gaba.
Jiya Litinin shugabannin Masar da Ethiopia da Sudan suka rattaba hanu kan yarjejeniyar a Khartoum.
Firayim Ministan Ethiopia Haile Marian Desalegn yace kasarsa zata ci gaba da aikin gina madatsan ruwa kan kudi dala miliyan dubu hudu, mataki da ya ce ba zai hana ruwan kogin gudu ba, duk da cewa sarsalar kogin na Nilu ya faro ne daga Kasar.