Masarautar Kano Ta Musanta Zargin Yin Zarmiya Da Aka Yiwa Sarki Sanusi II

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammad Lamido Sanusi ll

Musantawar na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ke kokarin gudanar da bincike dangane da zargin da ta samu akan sarkin.

Yayinda yake taro da manema labarai a fadar Sarkin, Walin Kano Alhaji Mahe Bashir Wali wanda kuma shi ne babban dan majalisar sarki mai kula da harkokin kudi na majalisar masarautar Kano.

Alhaji Bashir Wali yace rahotannin basu da tushe balantana ma makama. Yana mai cewa bayan binciken da suka yi sun fahimci cewa mai martaba Sarki na yanzu bai gaji Naira biliyan hudu ko shida ba.

Yayinda Sarki Ado Bayero ya rasu ya bar Naira biliyan biyu da miliyan dari takwas da casa'in da biyar da dubu dari da sittin da uku da wasu 'yan kai.

Kafin rasuwarsa an tadda Naira miliyan dari tara da tamanin da daya da dubu bakwai da tamanin da hudu da dari biyar da bakwai da kwabo saba'in da tara da aka yi anfani dasu aka biya ma'aikatan Ada Bayero City.

Abun da ya rage shi ne Naira biliyan daya da dubu dari takwas da saba'in da uku da dari uku da saba'in da takwas da dai sauransu su ne abun da sabon Sarki Sanusi ll ya gada.

Dangane da kudin da aka ce sarkin ya kashe wajen buga wayar tarho da kuma sha'anin sadarwa na internet Walin Kano yayi karin haske. Akan motocin sarkin yace abokanansa suka saya masa su.

Ka rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Masarautar Kano Ta Musanta Zargin Yin Zarmiya Da Aka Yiwa Sarki Sanusi II - 5' 29"