Sababbin dokokin da masarautar Brunei ta fito da su a kan hana zina da luwadi a kasar sun janyo wa kasar kulawar sauran kasashe dake nuna jin haushin daukar wadanan matakan.
WASHINGTON D.C. —
Sababbin dokokin da zasu soma aiki daga yau Laraba, sun tanadi hukuncin kisa a kan duk wanda aka kama da laifin aikata zina ko luwadi a kasar, kuma tuni aka saka sababbin dokokin a cikin jerin dokokin Shara’a da sarkin Musulmin Brunie, Sultan Hassanal Bokiah, ya kaddamar tun shekarar 2014.
Wadannan dokokin ance zasu yi aiki a kan kowa – ciki har da kananan yara da baki ‘yan wasu kasashen, kuma har a kan wadanda ma ba Musulmi bane.
Haka kuma dokokin sun tanadi tsinke hannun dama na duk wanda aka kama da sata, in kuma ya sake satar, a guntsure mishi kafar hagu.