Masar Ta Kafawa Hosni Mubarak Da Iyalansa Dokar Hanasu Tafiye Tafiye

Sojoji suke kallon dubban masu zanga zanga da suka hallara a dandalin Tahrir.

Babban mai gabatar da kara a Masar ya hana tsohon shugaban kasar Hosni Mubaraka da iyalansa daga barin kasar,kuma ya kwace dukiya da kadarorinsu a yayinda gwanati take binciken zargin cin hanci d a rashawa d a ake musu.

Babban mai gabatar da kara a Masar ya hana tsohon shugaban kasar Hosni Mubaraka da iyalansa daga barin kasar,kuma ya kwace dukiya da kadarorinsu a yayinda gwanati take binciken zargin cin hanci d a rashawa d a ake musu.

Ofishin babban mai gabatar da kara Abdel Meguid Mahmoud bai bayyana dalla-dalla bincikenda ake yi wa tsohon shugaban kasan d a iyalansa ba.Amma ofishin ya fada jiya litinin cewa dokar hana tafiye tafiyen ta shafi Mr. Mubarak,uwargidansa Suzanne,da ‘yayansu biyu da matansu.

Wan matakin yazo ne kwana daya bayan hukumomin sojin kasar suka hana matar Mr. Mubarak da karamin dansa Gamar daga tashi daga birnin yawo bude ido na Sharm el-Sheikh lokaicnda suka yi kokarinbarin Kasar. Babu bayanin ko dokar hana su fitar an kafa ne saboda sun yi kokarin barin kasar.

Jaridar Al-Ahram babbar jaridar kasar Masar ta jiya litinin, ta buga wani korafi da wani tsohon dan majalisar dokokin kasar,kuma mai sukar lamirin gwamnatin Mubarak d a ya bayyana dukiyar shugaban da iyalinsa.

Rahotannin kafofin yada labarai sun nuna abinda tsohon shugaban da iyalinsa suka mallaka ya kai dubban miliyoyin dalar Amurka.