Yau dinnan Lahadi, Rundunar Sojin Masar ta ce ta hallaka wasu ‘yan bindiga 16 sannan ta kama wasu da ake zargi su wajen sama 30 a wani aikin kakkabe ta’addanci wanda ta kaddamar a makon jiya, inda ta auna ‘yan ta’adda da sauran miyagu da kungiyoyinsu a fadin kas
Kafar labarai ta Reuters ta ce mai magana da yawun Rundunar Sojin, Kanar Tamer el-Rufai, ya fadi yau Lahadi cewa an auna motoci da makamai da na’urorin sadarwa da ma gonakin tabar sa maye ta opium a wannan aikin.
A wani jawabinta da aka yada ranar Jumma’a ta gidan talabijin, Rundunar sojin ta ce da sojoji da ‘yan sanda duk sun taka rawa a abin da ta kira “tsararren samame.”
Wannan aikin tsaron ya mai da hankali ne kan yankin Sinai mai fama da tashin hankali, inda a bara ‘yan bindiga su ka kai hari kan wani masallacin Sufaye, su ka kashe masu ibada wajen 311.