Akalla mutane 24 sun halaka, wasu fiyeda dari kuma sun jikkata wasu daga cikin su suna cikin mawuyacin hali, lokacinda jiragen kasa na fasinja biyu a Masar suka yi a karo kan hanyar zuwa birnin Alexandria mai tashar jiragen ruwa.
Wasu shaidun gani da ido suka ce daya daga cikin jiragen bai mutunta dokokin hanya ya afkawa jirgi na biyu.
Masu aikin kiwon lafiya masu aikin ceto sun bi ta cikin baraguzan jiragen biyu da suka yi karo kan babbar hanyar hanyar dogon kasar tsakanin Alkahira da birni na biyu a girma a kasar watau Alexandria.
Ministan sifiri na kasar Hisham Arafat ya isa inda aka yi hadarin jim kadan bayan aukuwarsa, yana tambayar 'Yansanda da kuma masu aikin ceto abunda ya faru.
Shi kuma kakakin ma'aikatar kiwon lafiya na kasar Dr. Khaleed Mujahed ya gayawa tasha r talabijin ta kasar cewa, ana kai wadnada suka jikkata asibitoci d a suke yankin.