Wannan na zuwa ne bisa la'akari da yadda ake ta samun karin sarakuna wadanda kuma mashawarta ne ga shugabanni wajen samar da ci gaba.
Koda turawan mulkin mallaka suka shigo yankin da ake kira Najeriya yanzu sun tarar da tsare-tsare na shugabanci wadanda ke gudana a lokacin wannan tsarin kuwa shine na sarakuna wanda ko bayan kafa mulkin mallaka a yankin arewa sun yi aiki tare da sarakuna.
Shugaba a majalisar sarakunan Najeriya, mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar wanda akai akai yana bayar da shawara ga mahukunta a Najeriya ya kara nada sarakuna 20 wasu daga cikin su tsofaffi ne yayinda wasu sabbi ne duk domin kara hada kan jama'a da kuma karfafa bayar da shawarwari ga shugabanni.
To sai dai wasu na ganin akwai sarautu masu muhimmancin da suka shafe shekaru babu wadanda ya dace a nada kamar yadda wani jinin sarauta ya shedawa muryar Amurka.
Ko bayan wannan akwai wasu kamar marafa da turaki da sallama wadanda ke da muhimmanci amma ba'a nada su ba, sai dai mai alfarma Sarkin Musulmi ya maganta akan sarautun da ba’a nada ba.
Da yake matsaloli suna ci gaba da yin tarnaki ga ci gaban Najeriya, abin jira a gani ko za'a gwada amfani da sarakuna domin dama su kansu, sun dade suna neman a kula da gudunmuwar da zasu iya bayarwa ko za'a samu fita daga matsalolin.
Saurara cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5