Masana Siyasa da Tsaro Na Fitar da Bayanan da Ka Iya Kawowa Najeriya Sauki

Barrister Solomon Dalung ministan wasa da matasa

Ana harsashen Najeriya zata fita daga matsalar tattalin arziki a wannan watan kuma da zara shugaban kasar ya dawo zai yiwa gwamnatinsa garambawul abun da minista Dalung shi ma ya fada tare da cewa satar da ake yi yanzu zata kawo karshe.

Ko babu makudan kudi masana harkokin siyasa da masana harkokin tsaro na fitar da bayanan da suke ganin zasu kawowa kasar saukin rayuwa mutane su zauna lafiya.

Baicin hakan akwai kuma harsashen kwamitin tattalin arziki dake cewa kasar zata fita daga halin tabarbarewa tattalin arziki wannan watan lamarin da zai kawo sassaucin rayuwa.

Su ko magoya bayan Shugaba Buhari na ganin da zara shugaban ya dawo zai yiwa gwamnatinsa garambawul domin "raba kara da kiyashi"

Barrister Solomon Dalung na ganin rashin kasancewar shugaba Buhari a kasar na sa wasu dake gwamnatin sakin hanya. Yace wata tsiyar da ake yi idan shugaban na nan babu mai soma aikatasu. Yace ko shugaban bai ce uffan ba babu wanda zai soma irin shegantakar.

Dalhatu Ribadu masanin tsimi da tanadi da ma'adanai yace idan 'yan siyasa na rage hadama za'a samu sassaucin kuncin rayuwa. Injishi zalunci ke kawo duk fitinar da ake gani. Yace an zabi mutum ko keke bashi dashi amma rana guda an saya masa motar Nera miliyan goma kuma talaka yana gani. Idan babu adalci kullum ana cikin wahala.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Masana Siyasa da Tsaro Na Fitar da Bayanan da Ka Iya Kawowa Najeriya Sauki - 2' 51"