Masana Shari'a na Tababar Cancantar Gwamnan Yobe da Shugaban Kasa Sake Tsayawa Zabe

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan da gwamnan Yobe Ibrahim Geidam su ne misalin wadanda suka saba layar kama aiki har sau biyu bayan wafatin iyayen gidansu wato shugaba Umar Musa 'Yar'Adua'a marigayi da kuma marigayi Sanata Manman Ali na Yobe

Hakan ta sanya masana shari'a da ma na kimiyar siyasa suke tababar cancantar wadan nan mutane biyu shiga zabe mai zuwa na 2015.

Malam Albati Bako wani masanin kimiyar siyasa a jihar Kano yace game da shugaba Jonathan kundun tsarin mulkin kasa ya nuna cewa za'a rantsar da shugaban kasa ne sau biyu shekara hurhudu shekara takwas ke nan. Wannan nan ma matsala ce da suke kallonta cewar la'alla akwai dar dar.

Farfasa Awal Hamisu Yadudu kwararren lauya ne kuma masanin kundun tsarin mulkin Najeriya. Shugaban kasa ko gwamna duk karbuwarsa ga jama'a ba zai iya yin mulki fiye da zango guda biyu ba. A fahimtarsu shugaban kasa mai ci bai cancanta ya sake tsayawa zabe ba domin ba'a yin zaben mataimakin shugaba. Tare suke fitowa neman zabe kuma shugaba ba zai iya tsayawa ba sai tare da mataimakinsa kamar yadda tsarin mulki ya tanada. Zaben 2007 da aka yi an zabesu ne tare da 'Yar'Addu'a a inuwa daya da riga daya.

Irin wannan fahimtar take karfafawa wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Yobe har ma suna neman alfarma daga wurin masu fada aji na jam'iyyar.

A wani taron manema labarai da suka kira a Kano kakakinsu Muhammed Gaskanta yace uwar jam'iyya ta kasa da ta jiha su yi masu adalci su duba halin da suke ciki. An samu shekara 16 yankin farko sun yi gwamna, yanki na biyu sun yi saura yanki na uku. Ya cancanta a taimaka masu a basu damar samun kujerar gwamna. A yi masu adalci. Gwamnan jihar yayi masu adalci kamar yadda suka sanshi da adalci.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Masana Shari'a Na Tababar Cancantar Gwamnan Yobe da Shugaban Kasa Sake Tsayawa Zabe - 3' 12"