Masana Na Fargaban Faduwar Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaban Najeriya Buhari

Biyo bayan faduwar farashen man fetur a kasuwar duniya masana na ganin idan ba'a yi hattara ba tattalin arzikin Najeriya ka iya durkushewa.

Muddin farashen man fetur ya cigaba da faduwa a kasuwannin duniya kuma Najeriya bata kirkiro wata hanyar samun kudin shiga ba ta musamman kuma masu yawa to tattalin arzikin kasar zai shiga wahala.

A cewar wasu masana yayinda kasashe kamar su China da Indiya da Japan ke cin ribar faduwar farashen man kasashen dake dogaro ga man fetur wurin samun kudin shiga kamar Najeriya da Venezuela da Rasha suna fuskantar matsaloli saboda rashin samun isassun kudin shiga.

Wani masani akan tattalin arziki Mr. Solomon Ayuba yace wasu dalilai da dama suka jawo faduwar farashen mai a duniya.Shigar Amurka cikin hakan man fatur ya sa ta rage sayen mai. Da Amurka ta fi kowace kasa a duniya sayen man fetur. Daga ita sai China.

Rage sayen man fetur da Amurka ta yi ya haddasa faduwar farashe. Abu na biyu kasashen da basa cikin OPEC basu da iyakar man da zasu haka sai ya sa suna cin karensu ba babbaka.

Kasafin kudin Najeriya na bana a yi shi ne akan farashen dalar Amurka hamsin da biyu kowace gangar mai. To amma sai gashi yanzu ma farashenta yana jele ne tsakanin dalar Amurka 45 zuwa 46.

Wato an samu gibin dalar Amurka shida a cikin kasafin kudin Najeriya. Wato idan kasar da hako gangar mai miliyan biyu kowace rana an samu gibin dalar Amurka miliyan 12 rana daya kawai.

Dole mahukuntan Najeriya u yi takatsantsan da kashe kudi su kuma daura damara sosai.

Ga rahoton Zainab Babaji da cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Masana Na Fargabar Faduwar Tattalin Arzikin Najeriya