Masana Na Ci Gaba Da Sharhi Kan Hukunce-Hukuncen Kotun Kolin Najeriya

Court hammer

A sharhin da ya gabatar game da bitar hukunce-hukuncen kotun koli akan zabukan wasu jihohi, lauya mai zaman kansa a birnin tarayya Abuja, Buhari Yusuf, ya ce lamarin shari’a na duba fiye da fuska daya don samun hukunci mai ma’ana.

Lauyan ya kuma ce ko da za a ga laifin manyan alkalan kotun kolin kasar, to in an yi nazari za a ga cewa akwai sashen kuskure daga lauyoyi ta hujjojin da su ka gabatar, ko mantuwa da su ka yi da abubuwan da za su iya ba su nasara. Yusuf yayi imanin cewa, alkalan na da kwarewar yanke hukunci kan kowacce irin shari’a mai sarkakiya kuma sun goge bisa aikin.

Masanin shari’ar ya kara da cewa, kotu kan ba mai shigar da kara abin da ya nema, kuma alkali ko da ya fahimci gaskiyar lamari, ba zai yanke hukunci da hakan ba sai dai bisa irin hujjojin da aka gabatar a zahiri. Ko da yake Lauyan ya ce alkalan mutane ne, don haka in sun yi kuskure akan wani lamari ba zai zama da mamaki ba.

Masanin shari'ar ya ce hukuncin jihohin Imo da Bayelsa da a ka yanke ya sha bamban da na Zamfara da za a koma kotun don ci gaba da nazari ko yanke hukunci ranar 17 ga watan nan.

Lauyan ya bukaci masu shigar da kara da su tanadi kwararan hujjoji kafin tunkarar kotu matukar suna son samun nasara.

Gakarin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Masana Na Ci Gaba Da Sharhi Kan Hukunce-Hukuncen Kotun Kolin Najeriya - 3'53"