Masana Kimiyya Sun Kirkiro Tabaran Leda Mai Laushi

Ga wadanda ba su ra’ayin sanya tabarau, ledar kan kwayar ido, wadda ake kira contact lense a turance, wani zabi ne mai burgewa. Amma masana kimiyya sun ma gano wata hanyar kara sa ta burgewa: ta yadda masu amfani da ita za su iya kura ido sosai da ita kan abin da su ke kalla, ta wajen kefta ido kawai sau biyu.

Masana kimiyya a Jami'ar California da ke birin San Diego a nan Amurka, sun kirkiro tabaran leda mai laushi, bayan da suka auna yawan wata sigina mai suna electrooculographic a turance, wadda a kan samu a duk lokacin da ido ya motsa - kamar sama da kasa, ko hagu da dama, da kuma keftawa. Ko a lokacin da ido ke a rufe, ko ana cikin bakin duhu, wadannan sigina kan faru.

Madugun wannan binciken, Shengqiang Cai, ya fadawa mujallar New Scientist cewa, “Mutane da dama na iya motsa kwayar idonsu har wannan sigina ta faru, ko da kuwa ba su iya ganin komai ”

Tabaran na leda, wanda masanan suka kirkiro, zai iya canza adadin gani bisa ga yawan siginar da ido ya haifar.