Masu nazari sun kirkiro da wani sabon gwajin jinni da ka iya taimakawa wurin gano cutar daji dake kama kundun dan adam wato “Pancreatic Cancer” a turance da wuri wuri, wannan cuta tana cikin cutauttuka mafi hadarin.
WASHINGTON D.C. —
Sau tari likitoci basu iya gano wannan cutar daji dake kama kundun dana dam har sai y agama illa. Akasari wadanda suka kamu da cutar suna mutuwa tsakanin shekara guda.
Sabuwar hanyar gwajin tana amfani da fasahar binciken kwayoyin jinni na mutane da saboda cutar sukari ko tarihin iyalinsu ke nuna zasu iya kamuwa da cutar dajin kundun.
Masu binciken sun ce an tabbatar da kashi 87 cikin dari da na ingancin sabon gwajin wurin gano matsayi na daya da na biyu na cutar dajin kundun kuma na yi nasarar samun kashi 98 cikin dari na kawar da cutar a jikin wadanda bata riga ta bugesu ba.