Kwararar Mabarata Jihar Kano Na Da Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya

Your browser doesn’t support HTML5

Masana harkokin tsaro a Kano dake arewa maso yammacin Najeriya sun yi gargadin cewa kwararowar mabarata cikin jihar daga jihohin makwabta da ke fama da matsalar tsaro, wata babbar barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.