Masana Harkokin Kasuwanci A Najeriya Sun Bai Wa Ngozi Shawarwari

Tsohuwar Ministar kudi a Najeriya, Dr Ngozi Okonjo-Iweala

Masana da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin kasuwanci da tattalin arziki a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da ba shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya, Ngozi Okonjo-Iwela shawarwari a kan yanda zata taimaka wa kasashen Afrika wurin yin cinikayya da sauran kasashen duniya.

A ranar Litinin din nan da ta gabata 1/3/2021 ne tsohuwar Ministar kudin Najeriyar kuma bakar fata ‘yar Afrika ta farko Ngozi ta kama aiki a matsayin shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya a birnin Geneva.

Kwamishinan Kudi na Jihar Neja, Alhaji Muhammad Zakari ya ce babbar shawarar shi ga Ngozin ita ce ta yi kokarin inganta cinikayyar man fetur a kasashen Africa.

Ya kuma bayyana damuwa a kan yanda kasashen Afrika ke aika kaya na matakin farko ba tare da sarrafa su ba, kamar danyen mai da Najeriya ke aikewa waje, abin da ya ce yana samar da ayyukan yi a wasu kasashe dama kudade masu yawa. A don haka ya yi kiran da a dau matakin kara wa kaya daraja kafin aika su, lamarin da ya ce zai kara yawan ayyukan yi a Afrika kana ya rage yawan tafiye tafiyen matasa.

Shi kuwa Alh. Muhammad Ahmad Kontagora wani kwararre a fannin kasuwanci a duniya ya ce sai ‘yan Afrika sun sanya gaskiya a harkokin kasuwancinsu kafin su ci moriyar aikin da Ngozin zata yi a matsayin shugaban Kungiyar Kasuwancin ta Duniya.

Ya ce babu wata nahiya a duniya da ta kai Afrika albarkatu da yawan filayen noma masu inganci amma galibin ‘yan kasuwa a Afrika musamman a Najeriya suna saka algusu cikin aikin da su ke yi. Ya ce kafin kasashen Afrika su ci gajiyar matsayin Ngozi kana su amfana da shirin kasuwancin bai daya na “Africa Free Trade Zone” sai sun daina saka ha’inci a harkokin kasuwanci.

Malam Yusuf Ladan Dan jarida ne kuma masanin harkokin kudi a Najeriya, ya ce duk da yana da yakinin sabuwar shugabar za ta taimaka wa kasashen Africa amma yana ganin tana da kalubale a gabanta.

A jawabinta na kama aiki, Ngozin tasha alwashin bin ka’idojin Kungiyar Kasuwancin ta Duniya ta yadda za ta samu nasarar bai wa ‘yan kungiyar hakkinsu domin biyan bukatunsu.

Ga dai rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna:

Your browser doesn’t support HTML5

Masana Harkokin Kudi Sun Baiwa Ngozi Shawara