Masana ta fuskar tsaro, sun shawarwaci jama’a su kara maida hankali, bayan da ‘yan binidga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka bullo da sabbin dabarun kai hare hare akan al’umma.
Sabbin hanyoyin sun hada da amfani da ‘ya’yan makiyaya, da makalawa yara nakiyoyi, idan suka koma gidajensu sai nakiyoyin su tashi, su haddasa barna mai yawa.
Saura sun hada da abunda suka saba yi, su kai hari- lokacin da mutane suka kawo dauki ga wadanda harin ya rutsa da su, sai su ta da wasu nakiyoyin domin halaka wadanda suka je ceto da kuma ‘yan kallo.
Wani tsohon jami’in tsaro, Mallam Usman Maraneyo , wanda ya zanta da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulazeez, ya ce akwai bukatar jama’a su kara kulawa da wurare da suke zuwa, da kuma irin wadanda suke mu’amala da su.
Shi ma a tasa gudumawar wani masanin harkokin tsaro Abu Mohammed, ya shawarwaci jama’a da su kara hankaltuwa, da wayewa, da fadada tunani kan mutane da suke hulda su.
Ya ce mutane su sa ido kan wadanda suke matsawa sai sun kutsa cikin taro, ko wani wuri da wata fitina ta tashi, domin irin wadannan mutanen, su ne mahara na biyu da suke zuwa da zummar haddasa mummunar barna bayan harin farkon.
Your browser doesn’t support HTML5