Maryam Ibrahim: Ina Gwagwarmayar Samawa Mata 'Yanci

Yau dandalinvoa ya sami bakuncin malama Maryam Ibrahim, Maryam dai malamar makaranta ce wacce ta karanci ilimin sanin masu aikata laifuka crime management prevention and control, bayan ta rasa samun gurbin karatu a fannin koyon aikin lauya sai aka bata shawarar ta karanta laifuffuka inda ta fara da diploma daga bisani ta sami degree inda ta kammala karatun ta.

Malama Maryam Ibrahim dai ta ce tana gwagwarmayar samawa mata ‘yanci ko damar da za a rika damawa da su a harkokin cigaban al’umma, kuma ta fara aiki ne a wani kamfanin sadarwa inda daga bisani data sami harkar koyarwa sai ta canza sheka.

Ta ce kalubalen da ta fuskanta bai taba sa ta gazawa ba ko jin tsoro tare da karaya, inda ta ce abu daya da take fuskanta bai wuce yadda wasu dalibai ke nuna rashin da’a da daraja malamai ba.

Daga karshe ta ja hankalin mata su jajirce wajen neman ilimi domin ilimi ne hanya daya tilo da ta ke daukaka mutum a dan kankanin lokaci.

Your browser doesn’t support HTML5

Maryam Ibrahim: Ina Gwagwarmayar Samawa Mata 'Yanci