Gwamnatin kasar Italiya ta fadada dokar takaita tafiye-tafiye a duk fadin kasar, inda ta killace mutum miliyan 60 a kokarin shawo kan yaduwar cutar Coronavirus.
WASHINGTON D.C. —
A wani Jawabin Frai ministan kasar, Giuseppe Conte wanda aka yada ta gidan talabijin jiya Litinin, ya ce wannan mataki na killace mutanen za a iya daukansa a matsayin “ina zaune ne a gida.”
Wannan mataki ya fadada dokar takaita zirga-zirga ta arewacin kasar inda aka fara samun barkewar cutar Coronavirus.
Mutanen da ke da dalilan aiki ko matsalar lafiya ne kadai za a iya bari su yi zirga-zirga tsakanin yankunan kasar Italiya ko zuwa wasu kasashen waje.
Frai minista Conte, ya ce “dole mu sauya dabi’unmu saboda mu yi naøarar shawo kan wannan cutar."
Italiya dai ta kasance daya daga aikin kasashen duniya da coronavirus ta fi addaba.