Martanin Gwamnatin Nijeriya Kan Rashin Zuwan Obama

  • Ibrahim Garba

Shugaba Obama da iyalinsa lokacin da ya sauka filin jirgin saman Dakar na kasar Senegal jiya Laraba

Gwamnatin Nijeriya ta ce rashin zuwan Shugaban Amurka Barack Obama Nijeriya a ziyarar kasashen Afirka da ya ke yi ba zai canza komai ba a dangantakar Nijeriya da Amurka.
Ministan Yada Labaran Nijeriya Mr. Labaran Maku ya ce rashin zuwan Shugaban Amurka Barack Oabama a ziyarar kasashen Afirka da ya ke yi ba zai canza komai ba a huldar Nijeriya da Amurka. Ya ce Shugabannin kasashe kan kai ziyara zuwa wasu kasashen ne bisa ga bukatar kasashen su. Don haka ba lallai ba ne Obama ya zo Nijeriya a wannan zagaye na ziyarar Afirka da ya ke yi.

Da ya ke bayani ga wakilin sashin Hausa a Fadar Shugaban Kasa Umar Faruk Musa, Ministan ya ce Nijeriya ce kasar da ta fi kasuwanci da Amurka a fadin Nahiyar Afirka kuma haka al'amarin zai cigaba da kasancewa duk kuwa da rashin zuwan Obama Nijeriya.

Mr. Labaran Maku ya ce 'yan adawa ne kawai ke kokarin alakanta rashin zuwan Obama Nijeriya da rashin kyan gwamnati saboda siyasa. Ya ce Nijeriya babbar kasa ce, don haka ba zai dace ba Obama ya zo Nijeriya ya yi dan mintoci kawai ya yi gaba kamar yadda ya ke yi a kasashen da ya ke ziyarta. Wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya yi nuni da yadda jami'an gwamnatin Amurka kan danganta rashin zuwan Obama Nijeriya da rashin yanayin tsaro mai kyau da sauran matsaloli.

Your browser doesn’t support HTML5

Martanin Gwamnatin Nijeriya Kan Rashin Zuwan Obama