Shugaba Muhammadu Buhari yayi jawabin cikar Najeriya shekaru 57 da samun ‘yancin kai daga turawan Birtaniya da suka yiwa kasar mulkin mallaka, inda shugaban ya lissafa irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannoni daban daban.
Akan yaki da cin hanci da rashawa wani kwararre Malam Muhammad I. Usman, a cikin firar da yayi da wakilinmu Umar Faruk Musa, yace “a zahiri ana samun nasara to amma nasarar kwarya kwaryan nasara ce” saboda wasu dalilan da ya lissafa.
Shima Malam Sha’aibu Idris, wani kwararre, a hirarsa da wakilinmu, yana ganin duk da nasarorin da shugaban ya ayyana an samu a harkokin tattalin arziki har yanzu talaka bai gani a kasa ba, duk kuwa da sanarwar da gwamnati ta bada na sanar da ‘yan kasa cewa tattalin arzikin ya fita daga masassharar da ya fada ciki, wato ya fara farfadowa.
Ga Umar Faruk Musa da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5