Martani Kan Kudirin Yin Garambawul a Dokokin Cututtuka Masu Yaduwa

Kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari da na masu kula da harkokin addini a Najeriya sun bukaci majalisar dokoki ta yi taka tsan-tsan wajen zartar da kudirin da zai yi garanbawul ga dokar tafiyar da bangaren cututtuka masu yaduwa a Kasar.

Tun a makon jiya ne majalisar wakilan Najeriya ta yi karatu na daya da na biyu akan wani daftarin doka da aka tsara zai yi garambawul ga tsarin kula da kiwon lafiyar al’umma a kasar, musamman lamuran da suka shafi dakile cututtuka masu saurin yaduwa a tsakanin jama’a.

Kwamrad Abdulrazak Alkali, daya cikin jagororin kungiyoyin rajin shugabanci na gari a Najeriya, ya ce ya kamata an duba kudurin sosai tunda ya shafi batun rigakafi na gama gari da kuma lafiyar al’umma.

Ko a makon jiya, a yayin wani taro na musamman akan batun yaki da cutar coronavirus, majalisar malamai ta kasa reshen jihar Kano ta tabo wannan batu na kudirin dokar kiwon lafiya da ke gaban majalisar dokokin kasar.

Dr. Saidu Ahmad Dukawa, sakataren majalisar malaman ya fayyace matsayar majalisar akan wannan batu, ya na mai cewa lallai majalisar kasa ta guji yin gaggawa wajen zartar da kudurin ba tare da jin ra’ayin jama’a ba, har sai an tabbatar babu wani abu mai cutarwa a tattare da matakin

A hannu guda kuma gwamnatin Najeriya ta bai wa hukumar lafiya ta duniya izinin yin gwajin wasu magunguna guda 4 na cutar coronavirus akan wadanda ke fama da wannan cuta a jihohin Kano da Kaduna, Sokoto, Lagos, Ogun da kuma babban birnin kasar Abuja.

Malam Kabiru Sa’idu Sufi, daya daga cikin masu sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriya. Ya ce abinda ya kamata shine a samu hadin kai tsakanin hukumomin gwamnati da kungiyoyin masu maganin gargajiya, shi ma ya ce bai kamata a yi gaggawa wajen karbar wannan gwajin rigafin da ake shirin yi ba.

Saurari karin bayani cikin sauti daga wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Martani Kan Kudirin Yin Garambawul a Dokokin Cututtuka Masu Yaduwa