'Yan Najeriya daga sassan kasar daban daban suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan shawarar da kanal Sambo Dasuki mai ritaya, wanda shine mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro ya bayar, na neman hukumar zabe ta dage zabe da za'a fara cikin watan gobe. Na baya bayan nan shine wadda kungiyar Limaman masallatan jumma'a dake jihar Niger suka yi.
A wani taron manema labarai da suka kira a Minna babban birnin jihar Alhamis din nan, shugaban kungiyar limaman, Imam Umar Farouk, yace gudanar da zaben ahalin yanzu shine mafi a'ala, saboda dage zaben babu abunda zai sauya, domin wadannan 'yan takarar dai sune zasu sake fitowa, kuma babu wanda ya san gobe sai Allah.
Shima da yake magana Imam Mohammed Aliyu Isa, na masallacin jumma'a dake kusa da makarantar horasda jami'an kiwon lafiya, yace dage zaben zai iya haifar da matsaloli wadanda ba za'a iya magance su, gara a yi yanzu domin an san matsalolin da ake fuskanta kuma ana iya daukar mataki akansu.
Limaman sun kuma yi alkawarin zasu rika amfani da hudubarsu domin fadakar da jama'a kan muhimmancin kaucewa tada fitina, koda kuwa sun lura cewa anyi zalunci.
Haka kuma Limaman sunyi ALlah wadai da mujallar nan ta Faransa mai suna Charlie Hebdo, wacce Limaman suka ce tayi patunci ga Manzo Allah. Duk da haka malaman suka ce, musulmi suka kai zuciya nesa, saboda Allah baya kyale wadanda suka muzanta Annabinsa.
Your browser doesn’t support HTML5