ZABEN2015: Manyan 'Yan Takarar Jam'iyyun PDP da APC sun Kara Kulla Wata Yarjejeniya

Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari.

Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari.

A yau ne akayi wata ganawa a babban birnin tarayya Abuja a karkashin kwamitin wanzar da zaman lafiya a lokacin siyasa a karkashin jagorancin shugaba Abdulsalami Abubakar, inda shugaba Goodluck Jonathan da Janar Mohammdu Buhari suka kara kulla wata yarjejeniyar zaman lafiya lokacin zabe.

Wannan yarjejeniyar dai ita ce ta biyu cikin kwanakin nan, inda tun farko kasashen waje suka hadu don duba hanyoyin da za a samar da zaman lafiya lokacin zabe.

Bayan haka kuma, yarjejeniyar ta baya-bayan nan ta kara jaddada muhimmanci amincewa da sakamakon zaben tsakanin ‘yan takarar, su kuma tabbatar da cewa kasar Najeriya ita ce kan gaba fiye da duk wani ra’ayi ko, sha’awa, ko maganar shugabanci.

‘Yan takarar dai sun sa hannu a yarjejeniyar inda suka kara bada tabbacinsu da amincinsu akan cewar babu gudu ba ja da baya, za su dauki duk matakan da ya kamata su dauka tsakanin su don tabbatar da cewa anyi zabe cikin ruwan sanyi haka kuma sakamakon da za a fidda zai zama amintacce ga kowannen su.

Yarjejeniyar dai ta zo ne bisa karin matsin lamba da ake ta cigaba da samu daga tarayyar turai da wasu kasashe na Afrika da suka ziyarci Najeriya kwanan nan don ganawa da duk ‘yan takarar don kara tabbacin samun zaman lafiya bayan zabe, kuma a tabbatar da cewa ba a kara samun irin tashe-tashen hankulan da suka faru a baya ba.

Amma kuma a dai-dai lokacin da ake yin wannan yarjejeniyar da kuma ganawar tsakanin ‘yan takarar biyu da kuma masu ziyarar Najeriya daga kasashen ketare dangane da samar da zaman lafiya a Najeriya, ba a gayyatar wadansu ‘yan takarar daga sauran jam’iyyu wadanda ake gani kanana ne.

Akan haka ne dokta Ibrahim Mani, dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar ADC wato Africa democratic congress ya yi korafin cewa kuskure ne a fifita wani dan takara fiye da wani, kamata yayi a ba kowa dama daidai gwalgwado ba tare da nuna bambanci ba don hakan na iya sa wasu su ga kamar za su yi duk abin da suka ga dama ba tare da an taka masu burki ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Manyan 'yan takarar jam'iyyun PDP da APC sun kara kulla wata yarjejeniya - 2'56"