Manyan Mawakan Hausa Na Duniya Zasu Yi Taro A Bauchi

A wannan makon ne ake kaddamar da gagarumin taron wakoki da laccoci na tsawon kwanaki uku na mawakan Hausa a Bauchi.

Jami’in yada labarai na wannan taron, Andy Bature, yace mawakan zamani da na gargajiya daga ciki da wajen Najeriya zasu halarci wannan taron, cikinsu har da Adam A. Zango, Aminu Ala, Fati Nijar, Nura M. Inuwa, Maryam Sangandale da sauransu. A cikin mawakan gargajiya, akwai Shehu Ajilo, Babangida Kakabori, magajin Danmaraya, Dankwairon Gombe da sauransu.

Abubuwan da za a gudanar sun hada da wasannin wakoki, da laccoci kan matsayin wakokin Hausa. Haka kuma mawaka masu sabbin wakoki zasu taho da su domin sayarwa a kan faya-fayen CD da MP3, har ma da tsoffin wakokin ga duk mai bukata.

Andy Bature yace za a gudanar da wasannin ne a babban filin wasannin gargajiya na Open Air Theater dake titin Ahmadu Bello Way a Bauchi, daura da kasuwar Wunti. Haka kuma za a gudanar da laccoci da wasu wasannin a babban dakin wasanni na Multipurpose Sports Hall dake kusa da nan.

Za a iya sauraron wadannan wasanni da kuma dukkan abubuwan da suke gudana lokacin wannan taro a wannan shafi namu na www.dandalinvoa.com kai tsaye a lokacin da suke gudana. Idan an bude shafin sai a duba kasa inda aka sanya alamar PLAY a matsa domin sauraron shirin kai tsaye.