Shugaban kungiyar Inter Milan, Guiseppe Marotta, ya tabbatar da sha'awar sayen dan wasa Victor Moses a karshen mako, inda yake cewa ba mamaki yarjejeniyar ta kankama da sauri.
Za’a bukaci kungiyar Fenerbahce ta amince da yarejejeniyar don takaita tsawon lokacin aron dan wasa Moses.
Chelsea, a shirye take ta yi kasuwanci muddin dai Inter ta sha alwashin sayar da shi da bazara akan kudi fam miliyan 10, wanda Inter din take bukatar gamsuwa da shi.
Tare da Olivier Giroud kuma suna da sha'awa, Antonio Conte ya dawo kungiyar gaba daya.
Kocin Kungiyar Chelsea, Frank Lampard ya yarda cewa mai yiwuwa dan wasan zai iya ficewa daga Stamford Bridge.
Lampard ya kara da cewar "Dan wasa Victor Moses, zai dawo daga aron da aka bada shi, kuma wannan tattaunawar tana gudana yadda ya kamata."