MInista a ma'aikatar kula da muhalli ta Najeriya, Alhaji Ibrahim Jibrin, Wamban Nasarawa, ya aza laifin dumamar yanayi kan manayan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki domin sune suke da masana'ntu, wadand zasu iya janyo haka.
Ministan wanda ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina, ya bada shawarar cewa, saboda haka ya zama wajibi, wadannan kasashen duniyan, su kawo gudumawa domin yaki da daukar matakai da suke janyo wannan matsala.
Haka nan, wasu suna aibanta kasashe kamar Najeriya, inda kamfanonin hakar mai a yankin Nija Delta suke kona iskar Gas.
Tsohon ministan harkokin mai Umaru Dembo, ya kare Najeriya kan wannan zargi, yana cewa ai ko wannan ma, kamfanonin na kasashen turan ne suke yin haka.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5