Muhammad Sambo Dasuki shi ne tsohon mai ba tsohon shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro.
Makonni biyu jami'an suka yiwa gidan kofar rago biyo bayan umurnin da shugaban kasa ya bayar na kama duk wadanda suke da hannu a kwangilar sayo makamai na fiye da nera miliyan dubu dari shida ko kuma biliyan dari shida.
Sauran wadanda kamun ya shafa sun hada da wasu hafsoshin soja na da da na yanzu da tsohon ministan tsaro Bello Haliru da tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa da Bashir Yuguda tare da shugaban gidan telibijan na AIT wato Raymond Dokpesi.
Bashir Baba mai sharhi akan lamuran yau da kullum yace dukiyar kasa ce an wawureta saboda yawancin mutane na korafin cewa tun da Buhari ya hau gadon mulki ba'a ga wani canji ba. Akan ko gwamnati zata iya zama lafiya bayan ta damke manyan mutane sai Bashir yace babu wani babba da ya fi karfin gwamnati. Dalili ke nan da yasa yakamata a samu gwamnati da zata nuna cewa babu wanda ya fi karfinta.
Masana shari'a irinsu Modibbo Bakari na ganin ba wai kawai kamun ne zai kayatar ba idan ba'a kafa kotu na musamman na yin shari'ar cin hanci da rashawa ba. Yace dole ne shugaba Buhari ya kafa kotun da zai mayar da hankali akan masu fuskantar zargin cin hanci da rashawa da almundahana cikin gaggawa. Idan ko ba haka ya yi ba zasu hada baki da wasu alkalai da wasu lauyoyi da zasu dinga jan shari'ar har karshen wa'adinsa. Yace akwai wadanda ake tuhumarsu a gaban kotuna tun kafin lokacin Obasanjo amma har yanzu ba'a gama shari'arsu ba kuma ba'a yi masu komi ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5