Manyan Hafsoshin Najeriya Sun Isa Borno Su Binciki Dalilin Hadarin Makon Jiya

Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

A Najeriya wata tawagar manyan hafsoshin dakarun sama na kasar sun isa jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar domin fara bincike kan yadda wani jirgin yakin kasar ya jefa bam-bamai biyu kan sansanin 'yan gudun hijira a makon jiya a wani kauye da ake kira Rann.

A kuma dai dai lokacinda rahotanni daga kamfanin dillancin Labarai na Associated Press yake nuni da cewa adadin wadanda harin bam-baman suka halaka ya rubanya zuwa 236.

Amma wata babbar jam'iar kungiyar kare hakkin BIl'Adama ta Human Rights Watch Mausi Segun tace tana da tsammanin cewa kwamitin binciken zai kunshi wakilai daga sassa daban daban ciki harda kungiyoyin fararen hula.

Kakakin rundunar sojin sama na Najeriya Ayodele Famuyiwa, ya gayawa Muryar Amurka cewa ana sa ran masu bincike zasu mika rahoton sakamkaon aikinsu nan da biyu ga watan gobe.

Wakilin Muryar Amurka Chika Odua ya aiko rahoto daga Abuja.